Da maraicen Lahadin nan,, Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya gudanar da wata ganawa ta musamman da mambobin tawagarsa da ma’aikata, a wani taro na sada zumunci mai taken “Maraice Ta Musamman Tareda Lamba Dayan Zariya .” Taron ya kasance an shirya shi ne domin ƙarfafa haɗin kai, goyon baya, da ɗaukar nauyin jagoranci tare.
Ganawar ta samar da yanayi mai natsuwa amma mai ma’ana, inda aka yi muhawara a fili, aka bayar da shawarwari masu amfani, da kuma nazari kan nasarori da ƙalubale, tare da tsara ingantacciyar hanya don kyautata shugabanci da ayyukan Karamar Hukumar Zariya.
Shugaban ya bayyana godiyarsa kan gaskiya da goyon bayan da aka nuna, ya karɓi gyara da shawarwari masu ma’ana, tare da jaddada ƙudurinsa na inganta ayyuka, ɗaukar alhaki, da bauta wa al’ummar Zariya yadda ya kamata.
Sanarwar da Jamin yada labarai a ofishin shugaban karamar hukumar Zaria Ishaq Galadima ya bayar ta ce taron ya kuma haifar da farkon tsari na faɗaɗa hulɗa da jama’a, ciki har da shirya tarukan jin ra’ayin jama’a (town hall meetings) domin bai wa al’umma damar bayyana matsalolinsu da bayar da shawarwari kai tsaye.
Taron ya samu halartar mamban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, manyan jami’an karamar hukuma, shugabannin jam’iyya, masu ba da shawara, da sauran manyan masu ruwa da tsaki.
Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Jaga) na ci gaba da nuna jajircewarsa wajen sauraro, haɗin gwiwa, da aiwatar da shugabanci mai maida hankali kan jama’a da ci gaba mai ɗorewa a Karamar Hukumar Zariya.











