Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Alhaji Abdulmutallab Sulaiman Goya, ya yi kira ga masu hannu da shuni da sauran al’umma da su rika tallafa wa marayu da masu buƙata ta musamman domin rage musu radadin rayuwa.Shugaban karamar hukumar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake kaddamar da shirin rabon tallafi da ya haɗa da rigunan sanyi, barguna, omo da sabulai ga marayu, masu buƙata ta musamman da kuma masu fama da lalurar tabin hankali a fadin karamar hukumar Funtua.Alhaji Abdulmutallab Sulaiman Goya ya bayyana cewa an samar da wadannan kayayyaki ne musamman domin tallafa wa marayu da suka rasa iyayen su tun suna kanana, yana mai cewa wannan shi ne karo na farko da aka tantance tare da zakulo marayu daga dukkan mazabun karamar hukumar domin amfana da irin wannan tallafi.Ya kara da cewa, kowane kansila a mazabarsa zai kaddamar da irin wannan shiri nan ba da jimawa ba, a matsayin wani bangare na kudirin gwamnatinsa na mayar da hankali wajen tallafawa marayu, masu buƙata ta musamman da gajiyayyu.Shugaban karamar hukumar ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta ba su damar nemo fili domin gina makarantar marayu a garin Funtua, inda ya tabbatar da cewa nan ba da dadewa ba, in sha Allahu, za a fara aiwatar da wannan aiki.Hakazalika, Alhaji Abdulmutallab Goya ya roki malamai da shugabannin addini da su ci gaba da yi wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, addu’a bisa irin ayyukan raya kasa da yake gudanarwa a karamar hukumar Funtua da ma jihar baki daya.A nasa jawabin, Mai ba Shugaban Karamar Hukumar Funtua shawara kan harkokin matasa, Honourable Aminu Halilu Yankara, ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar ya ba ofishinsa dama wajen sayo wadannan kayayyaki domin rabawa ga marayu, masu buƙata ta musamman da masu fama da lalurar tabin hankali.Ya ce yana da yakinin cewa wannan kudiri na tallafa wa marayu da Alhaji Abdulmutallab Sulaiman Goya ya assasa zai zamo sanadiyyar samun albarka, tsira da wadata ga wannan gwamnati, la’akari da falalar da ke tattare da tallafa wa marayu a addinin Musulunci.Kayayyakin da aka raba sun hada da:Omo kwali 250Sabulu kwali 250Rigunan sanyi guda 250Barguna guda 250Sanarwar da Jamin yada labarai Na karamar hukumar Bashir Yero ya bayar ta CE an zabo wadanda suka amfana ne daga mazabu goma sha daya (11) na karamar hukumar Funtua.A jawabansu daban-daban, Daraktan ESD, Alhaji Sulaiman Hassan, da Kansilan da ke kula da Ilimi, Jin Daɗi da Walwalar Jama’a na Karamar Hukumar Funtua, Honourable Nura Sani, tare da Welfare Officer, Alhaji Muhammad Lawal Kadisau, sun bayyana godiyarsu ga Shugaban Karamar Hukumar Funtua bisa kulawa da jajircewarsa wajen tallafa wa al’umma ta fannoni daban-daban.Sun kuma yi kira ga wadanda suka amfana da wannan tallafi da su yi amfani da kayayyakin yadda ya dace domin amfanin kansu






