Shugaban Karamar Hukumar Funtua Ya Kaddamar da Raba Kayan Abincin Azumi ga Mazabu 11.

mramalan10@gmail.com
3 Min Read

Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Alhaji Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya, ya kaddamar da rabon kayan abincin azumi da kudin cefane ga kwamitocin mazabu 11 da ke fadin karamar hukumar.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Alhaji Abdulmutallab Goya ya bukaci mambobin kwamitocin da su ji tsoron Allah tare da gudanar da aikin cikin gaskiya da rikon amana domin kayan su isa ga wadanda aka tanada domin su.

Wannan Na kunshe ne cikin wata sanarwar da Jamiin yada labarai Na karamar hukumar Funtua Bashir Yero ya bayar ga manema labarai.

Ya bayyana cewa kowace mazaba za ta karbi buhunan shinkafa 15 mai kilo 50, jarkoki uku na man girki mai lita 25, buhu guda na gishiri da buhu guda na kayan (Maggi), baya ga kudin cefane da za a bai wa kowace mazaba.

Shugaban ya kara da cewa an tsara rabon shinkafar ne domin a rika dafa buhu guda a kowace rana har na tsawon kwanaki 15, tare da rarraba abincin a kunshe cikin Takeaway ga marasa galihu, domin su samu saukin buda baki ba tare da wata wahala ba.

Alhaji Abdulmutallab Goya ya jaddada cewa wannan tsari ya samo asali ne daga manufar Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda wanda tun bayan hawansa mulki ya saba aiwatar da irin wannan shiri a duk lokacin watan Ramadan domin tallafa wa marasa karfi da gajiyayyu.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da yi wa kasa addu’a a wannan wata mai alfarma, yana mai cewa Allah (SWT) Mai karbar addu’ar bayinsa ne.

A nasa jawabin, Kansilan da ke kula da Sashen Ilimi, Jin Dadin da Walwalar Al’umma na Karamar Hukumar Funtua, Honarabul Nura Sani, ya bayyana cewa za a kawo sauran cikon abincin na kwana 15 nan ba da jimawaba kuma za a mikawa kwamitocin mazabu shinkafa da kayan hadin dafuwarta tare da kudin cefane, inda su kuma za su kula da dafa abincin da rarraba shi ga mabukata yadda ya kamata.

Ya kuma zayyana mambobin kwamitin kowace mazaba da suka hada da: Kansilan mazabar, Dagaci, Limaman Darika da na Izala, Shugaban Jam’iyya na mazabar da sauran masu ruwa da tsaki.

Share This Article
Leave a Comment