Hidimtawa Jamaa, Shugaban karamar hukumar Zaria Eng Jamil Jaga ya Halarci shagugulan daure aure da taaziyyar wasu da suka rasu a karamar hukumar.

mramalan10@gmail.com
3 Min Read

A ci gaba da hidimtawa jamaarsa, Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya gudanar da jerin ayyuka a unguwanni daban-daban na cikin karamar hukumar, inda ya halarci lokutan farin ciki tare da jama’a, tare da jajanta wa iyalai a lokutan jimami.

Shugaban ya fara hidimare ranar Asabar ce da halartar daurin auren Khadija, ‘yar Nasiru Shehu (Excellency), wadda aka daura aurenta da Hon. Yunusa Musa Ibrahim Giwa a Gidan Mal Danhanne, ,bakin kasuwa,Unguwar Karfe, gundumar Kaura.

Daga nan kuma ya wuce Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau, inda ya wakilci Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a wajen daurin auren Fatima da Ummu-Kulthum, ‘ya’yan Jarman Zazzau, Alhaji Mukhtar Ibrahim. Bikin ya samu halartar manyan sarakuna, ciki har da Sarakunan Lere da Jama’a, a gaban Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli, CFR.

Haka nan, Shugaban ya halarci daurin auren Rahma, ‘yar Alhaji Abubakar Maiwada, wanda aka gudanar a Gidan Mai Unguwa, Bishar, Kaura Ward, tare da halartar daurin auren Malam Anas Kwangero a Kwarbai “B” Ward.

A Tudun-Jukun Unity Quarters, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad ya samu karramawa ta zama Waliyin Amarya a daurin auren Maryam Danladi, ‘yar Alhaji Danladi Leader.

Haka kuma, ya tsaya a matsayin Wakilin Ango a daurin auren Tasi’u Muhammad Sani a Gidan Mai Anguwa, Hayin Dogo, Wusasa, Kufena Ward, sannan ya kuma tsaya a irin wannan matsayi a daurin auren Muhammad Sani (Mahmuda) da aka gudanar a Gidan Alhaji Adamu Aje, Limancin Kona.

Da yammacin Asabar din Kuma dai, Shugaban ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu, ciki har da ziyara zuwa Low-Cost, Gyallesu Ward, bisa rasuwar dattijo Alhaji Baban-Gimi, da kuma Unguwar Nupawa, Limancin Kona Ward, sakamakon rasuwar mahaifiyar Malama Fatima Abubakar.

Wadannan ayyuka na nuna kudurin Shugaban wajen kasancewa tare da al’umma a matakin tushe, ta hanyar rabon farin ciki da kuma tsayawa tare da su a lokutan bakin ciki.

Sanarwar da Jamin yada labarai a ofishin shugaban karamar hukumar Zaria Ishaq Galadima ya bayar,ya ce Injiniya Jamil Jaga ya yi addu’ar Allah Ya albarkaci dukkan sabbin ma’aurata da zaman lafiya da albarkar rayuwa, tare da rokon Allah Ya gafarta wa mamatan Ya kuma sanya su Aljannatul Firdaus.

TAGGED:
Share This Article
Leave a Comment