Muhawara akan kundin Bayanan Jeffrey Epstein da abubuwan da Ke biyo baya

mramalan10@gmail.com
2 Min Read

ibrahim makama, Kano.

Muhawarar da ake tafkawa a kafafen sada zumunta ta ci-gaba da ɗaukar zafi bayan sakin ƙarin sakonnin imel maaikatar shari’ar Amurka ta yi – waɗanda ake dangantawa da marigayi attajirin Amurkar nan, Jeffrey Epstein. Mista Epstein dai ya mutu ne yayin da ake tsare da shi a gidan kurkuku a 2019, inda yake fuskantar tuhuma kan safarar mata don yin lalata da su, kuma rahotanni sun nuna cewa akwai wata alaƙa ta ƙut-da-ƙut da yake da ita da manyan mutane a ɓangaren siyasa da kasuwanci.A baya-bayan nan, wasu saƙonni da ake yadawa a intanet na zargin aukuwar tattaunawa kan batutuwan binciken jikin ɗan Adam da kuma yiwuwar safarar mata daga Najeriya zuwa wasu ƙasashe. Cikin waɗanda ake ambatar sunayensu, har da attajirin nan Bill Gates, sai dai babu wata hujja ta hukuma da ta tabbatar da sahihancin waɗannan zarge-zarge.Masana harkar lafiya a Najeriya sun ce duk da rashin tabbas kan sahihancin saƙonnin, lamarin ya nuna muhimmancin tsauraran dokoki da sa ido kan duk wani binciken lafiya da ke da alaƙa da ƙasashen waje.Hankali ya kuma karkata ga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ministan Lafiya, Muhammad Ali Pate, inda ake kira da a ƙara bayyana hanyoyin sa ido, kare bayanan lafiyar ‘yan ƙasa, da tabbatar da cewa duk wani haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa yana bin dokokin Najeriya da ƙa’idojin duniya.Ƙungiyoyin farar hula da wasu ‘yan ƙasa na buƙatar ƙarin bayani daga hukumomi domin ƙarfafa amincewa da tsarin kula da lafiya, tare da tabbatar da cewa ana kare mata da ƙananan yara daga duk wata yiwuwar cin zarafi.Masana sun jaddada cewa neman bayani domin fitar da gaskiya ba abin zargi ne ba, illa wata hanya ta ƙarfafa riƙon amana da inganta tsarin samar da lafiya ga al’umma a cikin ƙasa.Ibrahim Makama Kano

Share This Article
Leave a Comment