‘Rijistar Ta Zamani Za Ta Ƙarfafa Shirye-shiryen Cin Zaɓe Na Jam’iyyar APC’
…”A Matsayina Na Jagoran Jam’iyya, Zan Ci Gaba da Shugabanci Mai Ma’ana Don mu Lashe Zaɓe Mai Zuwa” – Inji Gwamnan Gombe
…Ya Yi Gargaɗi Game Da Zagon Ƙasa, Tare Da Alƙawarin Ladabtar Da Masu Ƙoƙarin Rusa Haɗin Kan Jam’iyyar
Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya ƙaddamar da rajistar ƴaƴan Jam’iyyar APC na zamani a hukumance da kuma sake sabunta rajistar jam’iyyar a jihar, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa rajistar za ta ƙara ƙarfafa ikon jam’iyyar da kuma kaita ga sake samun nasara a zaɓe mai zuwa.
Gwamnan ya ƙaddamar da rajistar ce jim kaɗan bayan ya sake sabunta katinsa na kasancewa ɗan jam’iyyar a Sakatariyar Jam’iyyar APC na Jiha, inda jami’in Rijistar na Gundumar Jekadafari, Ukasha Hussaini ya yi masa rijista a gaban Shugaban Jam’iyyar APC na Gundumar, Alhaji Abubakar Muhammad Ɗan Gombe da sauran jami’ai.
Cikin sanarwar da babban daraktan yada labarai Na Gwabnan,Ismaila Uba Misili ya bayar,ya ce Gwabnan Ya bayyana aikin rijistar na zamani da sake
sabunta katin zama ɗan jam’iyyar a matsayin wani sabon abu mai muhimmanci wanda zai ƙarfafa jam’iyyar kuma ya nuna ainihin yawan ƴan APC a faɗin ƙasar nan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabannin APC na ƙasa bisa ɓullo da tsarin yin rijistar na zamani, yana mai cewa sanya lambar katin ɗan ƙasa, da katin zaɓe da tsohon katin Jamiyyar APC a matsayin muhimman buƙatun sabunta rajistar yana da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da sahihanci, gaskiya da kuma kishin jam’iyyar.
Ya yi ƙira ga ‘yan APC da magoya bayanta a faɗin Jihar Gombe su shiga yin wannar rajista sosai, kuma su yi amfani da damar samun katin APC na zamani don zama cikakkun ‘yan jam’iyya na ƙwarai.
Gwamnan ya tabbatar cewa an shirya duk wani abinda ake buƙata don tabbatar da nasarar rajistar, ba tare da wata matsala ba, kuma wanda zai shafi kowa a faɗin jihar.
Da yake jaddada ƙudurin APC na hidimtawa jama’a, Gwamna Inuwa Yahaya yace jam’iyyar tana ci gaba da maida hankali kan samar da shugabanci nagari da ci gaba mai ɗorewa.
Yace a ƙarƙashin Jam’iyar APC, gwamnatinsa ta cimma manyan nasarori, waɗanda suka canza yanayin zamantakewa da tattalin arziƙi da ababen more rayuwa na Jihar Gombe.“Aƙidar gwamnatinmu ta APC ita ce inganta yanayin jiharmu fiye da yadda muka sameta.
Duk wanda ke da shakku game da wannan batu ya waiwaya baya ya yi nazari game da yanayin da Jihar Gombe ke ciki a lokacin da muka hau mulki kimanin shekaru bakwai da suka gabata don ya fahimci irin ci gaban da muka samu,” in ji Gwamnan.
Gwamna Inuwa Yahaya yace ba a kai ga samun nasarorin da aka cimma ba sai da goyon baya, haɗin kai da ƙarfafa gwiwa daga APC da al’ummar Jihar Gombe.Ya bayyana jam’iyyar a matsayin mai ƙarfi daga mai tushe a fagen siyasar jihar, yana mai tabbatar da cewa a matsayinsa na jagoran jam’iyyar a jihar, zai ci gaba da samar da shugabanci mai ma’ana don samun gagarumar nasara a zaɓen dake tafe.
Ya ƙara da cewa yin rijistar membobin na zamani da sake sabunta katinta zai ƙara ƙarfafa ikon APC na tsayawa takara da cin zaɓe a kowane mataki.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗi mai tsanani ga mutanen dake da niyyar haifar da ɓaraka a cikin jam’iyyar, yana mai jaddada cewa shugabannin APC ba za su yi wata-wata ba wajen ɗaukar matakan ladabtarwa kan duk wanda aka samu yana zagon ƙasa ga haɗin kai da kwanciyar hankalin APC a jihar.
Tun da farko, Shugaban Jam’iyyar ta APC a Jihar Gombe, Mista Nitte Amangal, ya bayyana cewa yin rijistar membobin na zamani da sake sabunta shi, na da nufin ƙarfafa tushe, da ƙara yawan ƴaƴan jam’iyyar da kuma inganta tsarinta kafin babban zaɓen 2027.
Yace sabunta rajistar da Gwamnan ya yi, ta alamta fara aikin gadan-gadan a duk faɗin jihar, yana mai ƙira ga membobin jam’iyyar a dukkan matakai su fito su yi rijistar yadda ya kamata.









