Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria, Engr. Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya halarci taron Kwamitin Raba Asusun Ƙananan Hukumomi na Jihar Kaduna (JAAC) na watan Disamba, 2025, taron dai na bisa tsarin doka, Kuma ya na mayar da hankali kan daidaita harkokin kuɗi, gaskiya, da ingantaccen amfani da kudaden gwamnati.
An Yi Taron ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi, Hon. Sadiq Mamman Lagos, tare da halartar Babban Sakataren Ma’aikatar, Dr. Mahmud Lawal, shugabannin ƙananan hukumomi jihar Kaduna su 23, da daraktoci, da wakilan hukumomin gwamnati da suka haɗa da SUBEB, RUWASSA, Ofishin Akanta-Janar, PHCB, Hukumar Fansho, da Hukumar Ayyukan Ƙananan Hukumomi.
An gudanar da taron a Dakin Taro na Sanata Uba Sani dake sakatariyar maaikatar kula da kananan hukumomi na jihar Kaduna , inda aka duba rabon kuɗaɗe, da nauye nauyen kudaden kananan hukumomin, da daidaita tsare tsaren kashe kudinsu tare da laakari da bukatun ci gaban al’umma a matakin ƙasa.Halartar Shugaban Ƙaramar Hukumar Zaria a taron ya ƙara jaddada ƙudurin gwamnatinsa na riƙon amana, rashin wasa da aiki da tsare-tsare masu inganci, da kyakkyawan shiri.
Sanarwar da Jamin yada labarai Na ofishin shugaban karamar hukumar Zaria Ishaq Galadima ya bayar ya ce ana sa ran shawarwarin da aka cimma za su inganta ayyukan Alheri da karamar hukumar ta tsara aiwatarwa a Zaria, musamman a fannonin ilimi, lafiya, samar da ruwa, jin daɗin ma’aikata, da ayyukan ci gaba.






