Ayyukan Alheri,da Taimakon Jamaa su me Eng Jamil Jaga ya sa a gaba.…..

mramalan10@gmail.com
2 Min Read

..Mata da matasa da Masu karamin karfi a Zaria Sai hamdala …

Kamar Yadda ya Saba, Shugaban Karamar Hukumar Zariya, Injiniya Jamil Ahmad Muhammad (Jaga), ya sake jaddada tsayuwar daka da kudurin gwamnatinsa na aiwatar da shugabanci na bunƙasa ci gaban al’umma daga tushe, ta hanyar shirya Shirin Ƙarfafa Matasa da Mata da aka gudanar a Zariya.

A karkashin wannan shiri, sama da mutum 250 daga gundumoni 13 na Karamar Hukumar sun amfana da tallafin kuɗi domin ƙarfafa ƙananan sana’o’i, inganta rayuwar al’umma, da kuma rage raɗaɗin rayuwa .

An raba tallafin kuɗin ne kamar haka: ₦𝟱𝟬𝟬,𝟬𝟬𝟬, ₦𝟮𝟱𝟬,𝟬𝟬𝟬, ₦𝟮𝟬𝟬,𝟬𝟬𝟬, 𝗱𝗮 ₦𝟭𝟬𝟬,𝟬𝟬𝟬, domin tabbatar da cewa kowane mai cin gajiyar shirin ya samu tallafi bisa la’akari da buƙatarsa.

An samu nasarar aiwatar da wannan muhimmin shiri ne sakamakon ci gaba da goyon baya da jagoranci nagari na Mai Girma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani , CON, wanda manufofinsa na jin ƙai da sauƙaƙa rayuwar al’umma ke ci gaba da haifar da gagarumin amfani a matakin ƙasa.

Wadanda suka amfana da shirin sun bayyana matuƙar godiya ga Shugaban Karamar Hukumar bisa jajircewarsa, tare da gode wa Gwamna bisa samar da irin waɗannan tsare-tsaren da ke sauya rayuwa.

Wannan shiri ya sake nuna akida JAGA cewa ƙarfafawa da tallafa wa al’umma, ba alkawura kawai ba, shi ne ginshiƙin samun ci gaba mai ɗorewa a Karamar Hukumar Zariya.

Share This Article
Leave a Comment